Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta sanar da dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara tana bai wa gwamnatin tarayya wa’adin wata ɗaya don kammala tattaunawar sabunta yarjejeniyar 2009 da warware sauran matsalolin da ke addabar jami’o’in ƙasar.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abuja, inda ya ce an yanke wannan shawara bayan tattaunawa mai amfani tsakanin ASUU da gwamnati, tare da shiga tsakani daga majalisar dattawa.
Farfesa Piwuna ya tuna cewa ƙungiyar ta shiga yajin aikin gargadi tun ranar 13 ga Oktoba, 2025, sakamakon jinkirin gwamnati wajen magance batun yarjejeniyar 2009 da sauran buƙatu masu muhimmanci da suka shafi jin daɗin malamai.
Ya ce bayan fara yajin aikin, gwamnati ta sake kulla tattaunawa da ASUU ta hannun tawagar da Alhaji Yayale Ahmed ya jagoranta, inda aka gudanar da tarurruka a ranar 16 da 18 ga Oktoba don duba amsar gwamnati ga yarjejeniyar da aka sake tsara.
Labari mai alaƙa: Yajin Aiki: Majalisar Dattawa ta fara sulhunta tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya
Shugaban ya bayyana cewa, ko da yake ba a warware dukkan matsaloli ba, an samu ci gaba mai ma’ana fiye da lokacin da ake gabanin yajin aikin, kuma hakan ya nuna cewa da gwamnati ta amsa da wuri, da ba a shiga yajin aikin ba.
ASUU ta yaba da gudunmawar kwamitocin majalisar dattawa kan ilimin gaba da sakandare da TETFund da ma’aikata, da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, bisa kokarinsu na sulhu.
Ƙungiyar ta ce majalisar zartarwarta ta ƙasa ta gudanar da zama daga 21 zuwa 22 ga Oktoba, 2025, inda ta amince da dakatar da yajin aikin domin ba da damar ci gaba da tattaunawa.
Duk da haka, ta gargadi gwamnati da cewa idan ta kasa kammala warware matsalolin cikin wata guda, za ta dawo da yajin aiki ba tare da wani sabon gargadi ba.













































