Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma (CITAD) ta yi Allah-wadai da kama wasu matasa biyu a ƙaramar hukumar Tofa ta jihar Kano bisa zargin su da wallafa rubutu a Facebook da ke nuna suka kan shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Ibrahim Yakubu Addis, saboda watsi da aikin ginin hanya a yankin.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mutanen da aka kama, Murtala Garba Doka da Shamsu Safiyanu Lambu, an cafke su ne a ranar Litinin bisa umarnin shugaban ƙaramar hukumar bayan wallafar da suka yi kan hanyar Lambu–Banki–Yarimawa–Jakata, wadda gwamnatin jiha ta amince da ta kashe naira miliyan 240 domin gina ta.
A wata sanarwa da daraktan CITAD, YZ Ya’u, ya fitar a Kano a ranar Laraba, ta bayyana cewa an tsare matasan a ofishin ‘yan sanda na Tofa kafin daga baya a tura su hedikwatar ‘yan sanda na jihar Kano da ke Bompai don ci gaba da bincike.
Sanarwar ta bayyana cewa kamun matasan ya janyo tashin hankali a cikin al’umma, tare da nuna cewa hakan na cikin wata mummunar dabi’a da ke ƙara yawaita na tsoratarwa da keta ‘yancin ‘yan ƙasa da masu amfani da kafafen sada zumunta, duk da suna aiwatar da haƙƙin su na faɗar albarkacin baki.
CITAD ta bayyana cewa kama mutane saboda bayyana ra’ayoyinsu kan ayyukan gwamnati babban take haƙƙin ‘yancin ɗan adam da sashe na 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada, da kuma ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da Najeriya ta sanya hannu a kai.
Cibiyar ta bukaci a saki Murtala Garba Doka da Shamsu Safiyanu Lambu ba tare da wani sharadi ba, tare da kira ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ta guji bari a yi amfani da ita wajen cin zarafin jama’a ta fuskar siyasa.
Sanarwar ta kuma ja hankalin jami’an gwamnati da su rungumi gaskiya da karɓar suka a matsayin ginshiƙan dimokuraɗiyya, tare da ƙarfafa masu amfani da kafafen sada zumunta su ci gaba da amfani da haƙƙinsu cikin natsuwa wajen ƙara bayyana gaskiya da tabbatar da ingantaccen mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.













































