Wata babban kotu da ke zama a jihar Enugu, ta yanke hukuncin daurin shekaru 304 ga Mista Emmanuel Sombo a dalilin laifin satar kudi.
Vanguard ta rawaitu cewa a ranar Talata, ya nuna cewa Alkali Kenneth Okpe ya samu Emmanuel Sombo da laifin da EFCC take tuhumarsa. Ana zargin Mista Sombo ya yi amfani da takardu ya saci N34.9m daga asusun kwalejin koyar da ilmi ta tarayya da ke Eha-Amufu a jihar Enugu.
Wanda ake tuhuma shi ne Akanta a wannan makaranta, tun shekarar 2010 yake shari’ar da hukumar EFCC a wata kara mai lamba E/56C/2010 a kotu.
Ana zargin Akantan ya yi irin sa hannun shugabannin makarantar tarayyar domin cire kudi daga asusunsu da ke wani banki domin yin hidimar gabansa.
Shugabannin kwalejin a lokacin wanda suka hada da Shugaba, Magatakarda da Mai kula da kudi duk musanya sa hannu a kan takardun cire kudi a bankin.
Mai shari’a Kenneth Okpe ya ce ya gamsu cewa Emmanuel Sombo ya yi amfani da sa hannun ma’aikatan, ya cire kudi da sunansu. Alkalin ya ce kotu ta karbi hujjojin da masu shigar da kara suka bada, don haka ya kama wanda ake zargi da duk jerin laifuffukan da EFCC take zarginsa.













































