Gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin Sadarwa dasu soke karin kaso 10 na kiran waya dasu kayi

NCC

Gwamnatin Tarayya ta umurci Ma’aikatan Sadarwa ta kasa da ta sauya gyare-gyaren farashin kiran waya na bai-daya.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Oktoba 12, ta bada wannan umarni ne biyo bayan rahotannin kafafen yada labarai na aiwatar da tsarin bai daya na kashi 10 cikin 100 da aka amince mu su kwanan nan.

Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, Dr Reuben Muoka, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Muoka ya ce, la’akari da amincewar kashi 10 cikin 100 ya yi daidai kan ka’idojin hukumar sadarwa ta Najeriya ta tanadar.

Ya kuma yace hakan ya yi dai-dai da sauran ka’idoji domin hakan yana cikin tanadin kayyade farashin da ake da shi kamar yadda aka kayyade wa masana’antar.

Ya ce an dauki matakin ne bayan nazari mai tsauri, nazarin yanayin aiki da yanayin kasuwanci a Najeriya, domin ya shafi dukkan bangarorin tattalin arziki.

Ya ce Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na kasa Farfesa Isa Pantami ya tabbatar da cewa abin da ya sa a gaba shi ne kare ’yan kasa da tabbatar da adalci ga duk masu ruwa da tsaki da abin ya shafa.

Ya rawaito ministan yana cewa: “Saboda haka, ba za mu amince da duk wani abu da zai kara kawo wahalhalu a wannan mawuyacin lokaci ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here