Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu bai gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a kasar Faransa ba.
A wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ofishin yada labaran Tinubu, Tunde Rahman, ya bayyana rahotannin da aka bayar na shirin haduwar Tinubun da Wike a matsayin labaran karya, don haka ya bukaci al’umma da su yi watsi da shi.
Idan dai za a iya tunawa, wasu kafafen yada labarai sun bada rahoton ganawar da ake zaton za a yi tsakanin Tinubu da Wike, jigo a jam’iyyar adawa ta PDP.












































