WASSCE 2026: WAEC ta rike sakamakon dalibai 167,486

WAEC

Kimanin dalibai miliyan 1.2 daga cikin miliyan 1.95 da suka rubuta jarrabawar kammala sakandire ta kasashen Yammacin Afirka ta amfani da na’ura mai kwakwalwa (CB-WASSCE) sun samu maki mai kyau akalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

Shugaban hukumar WAEC na Najeriya, Dr. Amos Dangut, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake sanar da sakin sakamakon jarabawar a Lagos.

A cewarsa, daga cikin dalibai 1,950,726 da suka rubuta jarabawar a Najeriya, an kammala aiki da sakin sakamakon dalibai 1,834,695, wanda ke wakiltar kashi 94.05.

Ya ce an rike sakamakon dalibai 167,486, wanda ke wakiltar kashi 8.59 na wadanda suka rubuta jarabawar CB-WASSCE ta 2026, saboda zargin yin magudin jarabawa.

Ya kara da cewa har yanzu ana aiki kan wasu daga cikin darussan dalibai 116,031, wanda ke wakiltar kashi 5.95, saboda wasu matsalolin da ake magancewa a halin yanzu.

Dangut ya tabbatar wa daliban da abin ya shafa cewa ana kara kokari domin kammala aikin da fitar da sakamakon da ya rage cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

A kan bayanin yadda dalibai suka yi, ya ce dalibai 1,687,378, wanda ke wakiltar kashi 86.50, sun samu nasara a akalla darussa biyar, da Turanci da Lissafi ko ba tare da su ba.

Ya kuma bayyana cewa dalibai 1,200,514, wanda ke wakiltar kashi 61.54, ne suka samu nasara a akalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here