Muhimman sauye-sauye da ya kamata ku sani game da gyaran da aka yi wa NYSC karo na farko a tarihi

NYSC NYSC 750x430

Shugaba Bola Tinubu ya amince da cikakken garanbawul ga Tsarin Hidimar Kasa (NYSC), wanda shi ne gyara na farko mai girma da aka yi wa tsarin tun shekaru da dama.

A karkashin sabon tsarin, farar hula ne zai jagoranci ayyukan NYSC na yau da kullum, yayin da sojoji za su ci gaba da baiwa masu hidimar kasar tsaro da goyon bayan a fadin kasar.

Shugaban Kasa ya kuma ba Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi da Ministan Matasa, Ayodele Olawande, umarnin su gyara Dokar NYSC da dokokinta domin tabbatar da gyare-gyaren da aka amince da su da kuma saukaka aiwatar da su nan take.

Ga manyan sauye-sauye bakwai da ya kamata ku sani gme da gyara

1. Tsarin kira na dijital

Za a yi amfani da tsarin kira na dijital gaba daya domin tabbatar da inganci, gaskiya da inganta aikin.

2. Lura da yanayin tsaron don kare su daga hadari

Za a tura ‘yan kasa zuwa wuraren hidima bisa kimantawa yanayin tsaro domin inganta tsaron su a lokacin hidima.

3. Sabon tsarin sansanin koyo

Za a mayar da hankali sosai a sansanin koyo na makonni shida kan habaka jagoranci, kasuwanci, fasahar dijital, da kuma fannonin sana’o’i na musamman.

4. Gudanar da hidima bisa abin da mutum ya kware

Za a tura masu hidimar zuwa cibiyoyi da suka fi dacewa da abin da suka karata.

5. Shirye-shiryen jagoranci na farar hula

Farar hula ne za su gudanar da ayyukan NYSC na yau da kullum, yayin da sojoji za su ci gaba daukar nauyin samar da tsaro.

6. Ingantattun ka’idojin sansani

Za a kafa tsarin tantancewa da ba da takardar sheda na kasa domin inganta darajar sansanonin koyo a fadin kasar.

7. Sabon bikin kammalawa da sabon kaya

Za a maye gurbin bikin yayewa na gargajiya da bikin kammala karatu, yayin da za a baiwa masu hidimar sabon kayan NYSC da aka tsara domin nuna kwarewa da alfaharin kasa.

Ana sa ran wadannan gyare-gyaren za su zamanantar da tsarin Yi Wa Kasa Hidima, su inganta tsaro da damar samun aiki a ‘yan kasa, da kuma daidaita shirin da bukatun zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya da ke canzawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here