Gwamnatin Kano ta musanta bayar da umarni hawan Sallah 

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata jita-jitar da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai da kuma kafafen sada zumunta cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci hawan Sallah.

Gwamnatin ta bayyana cewa rahoton ba shi da tushe, tare da ƙara da cewa babu wata hukuma da ta yanke hukunci kan batun har zuwa yanzu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa rikicin sarautar Kano na gaban kotu a halin yanzu, don haka ya zama dole a bar bangaren shari’a ya gudanar da aikinsa ba tare da wata matsin lamba ko rikicewar da jita-jita ke haifarwa ba.

Karanta: Gwamnatin Kano ta rushe wasu gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a Sharada, ta gargadi masu gine-ginen

A halin yanzu, gwamnatin jihar ta sake nanata cewa tana tsaka-tsaki, kuma ta nesanta kanta daga kowanne bangare na rikicin sarautar har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe da doka ta amince da shi.

Gwamnatin ta kuma bukaci jama’a da su kasance masu bin doka, su guji yaɗa jita-jita, tare da tabbatar da cewa suna samun bayanai daga sahihan hanyoyi na hukuma kawai.

Haka kuma ta gargadi kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin yaɗawa, domin kauce wa haifar da rudani ko tashin hankali a cikin al’umma, musamman yayin da bukukuwan sallah ke gabatowa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here