Tsohon gwamnan Jihar Benue kuma sanata, Gabriel Suswam, ya fice daga jam’iyyar PDP, inda ya ajiye membobinsa na jam’iyyar a ranar Laraba.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya sanya wa hannu da kansa, wadda ya aike wa mazabar Mbagber a ƙaramar hukumar Logo ta jihar, kuma aka fitar da ita ga manema labarai a Makurdi.
Suswam ya bayyana cewa bai yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar cikin sauƙi ba, yana mai cewa jam’iyyar PDP ta ba shi damammaki da dama a baya domin yi wa jihar da ƙasa hidima.
Ya jaddada cewa tsawon shekaru jam’iyyar PDP ta ba shi dama ya yi aiki a fannoni daban-daban, ciki har da zama ɗan majalisar wakilai, gwamnan Jihar Benue da kuma sanata a Najeriya, yana mai nuna godiya kan amincewar da aka nuna masa a lokuta daban-daban.
Tsohon gwamnan mai wa’adi biyu ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a halin yanzu na fama da rikicin cikin gida da ba ya ƙarewa, inda ya ce duk ƙoƙarin da masu fatan alheri suka yi domin warware rikicin ya ci tura.
Ya ƙara da cewa rikice-rikicen shugabanci, tsari, ladabi da akida sun dabaibaye jam’iyyar ba tare da wata hanya bayyananniya ta warware su ba, lamarin da ya sa jam’iyyar ke ci gaba da kasancewa cikin matsanancin rikici.
Suswam ya ce a matsayinsa na mai kishin dimokuraɗiyya, ya kasa daidaita ci gaba da kasancewarsa a jam’iyyar PDP da ra’ayoyinsa na siyasa da burinsa na bayar da gudummawa mai ma’ana ga gina ƙasa a cikin tsayayyen tsarin siyasa.
Ya tabbatar da murabus dinsa tare da yi wa jam’iyyar fatan alheri idan ta samu damar warware matsalolinta na cikin gida nan gaba.
NAN













































