Kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta bayar da beli ga kwamishinan kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, da wasu mutane uku da ake tuhuma da hannu wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci da kuɗi har Dala Miliyan 9.7.
Kotun ta umarce su da su ajiye Naira Miliyan 400 gaba ɗaya, wato naira miliyan 100 kowannensu.
Mai shari’a Mohammed Umar ya shimfiɗa sharuddan belin da suka haɗa da gabatar da mutane biyu masu tsaya musu a kan kowane wanda ake tuhuma, inda ɗaya dole ya kasance babban sakatare mai aiki a gwamnati, ɗayan kuma darakta mai aiki a ma’aikatar gwamnati.
Haka kuma kotun ta umarce su da su miƙa fasfo na ƙasashen waje tare da hana su fita daga ƙasa sai da izinin kotu.
Kotun ta kuma wajabta musu riƙa kai rahoto ofishin Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa DSS da ke Bauchi duk ranar Litinin, tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga Maris domin ci gaba da shari’ar.
Yakubu Adamu, tsohon manajan reshen Polaris Bank a Bauchi, an gurfanar da shi a gaban kotu a ranar 31 ga Disamba tare da wasu ma’aikatan gwamnati uku da suka haɗa da Balarabe Abdullahi Ilelah, Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed, bisa tuhume-tuhume 10 da suka shafi haɗin baki, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da tallafa wa ta’addanci.
A wani hukunci da mai shari’a Emeka Nwite ya yanke a ranar 5 ga Yuni, kotu ta ƙi bayar da beli ga waɗanda ake tuhuma bisa dalilin cewa laifukan da ake tuhumar su da su na barazana ga tsaron ƙasa da zaman lafiyar al’umma.
Karanta: Zargin ta’addanci: Kotu ta bayar da umarnin kama waɗanda ake zargi da alaƙa da Bello Turji
Kotun ta bayyana cewa sakin su kafin shari’a na iya jefa jama’a cikin hatsari, duk da tanadin kundin tsarin mulki da ke ɗaukar mutum a matsayin marar laifi har sai an tabbatar da laifinsa.
Sai dai a hukuncin da aka yanke daga baya, mai shari’a Mohammed Umar ya bayyana cewa bangaren masu gabatar da ƙara bai gabatar da hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa waɗanda ake tuhuma za su tsere ba, lamarin da ya sa kotu ta ga dacewar bayar da beli a yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Gwamnatin tarayya na zargin cewa a tsakanin Janairu da Mayu na 2024, Yakubu Adamu tare da babban akanta na jihar, Sirajo Jaja, Samaila Irmiya Liman da sauran waɗanda ake tuhuma, sun bai wa Bello Bodejo da mutanen da ke da alaƙa da shi kuɗi har dala miliyan 2.3 a hannu, ba tare da bin tsarin cibiyoyin kuɗi ba. Bello Bodejo shi ne shugaban Miyetti Allah Kautal Hore, wanda aka taɓa kama shi bisa zargin ta’addanci.
A cewar gwamnati, an bayar da waɗannan kuɗaɗe ne duk da sanin cewa za a iya amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci, inda aka ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da ake zargi ciki har da babban akanta na jihar na gudun hijira.
Duk da haka, waɗanda ake tuhumar sun musanta laifukan da ake zarginsu da su, tare da neman kotu ta barsu a waje har sai an kammala shari’ar.













































