A ranar Laraba ne babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama, Abuja, ta sanya ranar 10 ga watan Disamba, domin yanke hukunci kan bukatar belin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya shigar.
SolaceBase ta ruwaito cewa, Bello, tare da wasu mutane biyu, Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu, suna fuskantar shari’a a gaban hukumar kula da harkokin tattalin arziki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, bisa zarge-zargen cin amana da hada baki wajen aikata laifukan da suka kai Naira biliyan 110.4.
Alkalin da ke jagorantar shari’ar, -Justice Maryann Anenih ta bayyana ranar bayan masu gabatar da kara da kuma lauyan da ke kare su sun yi muhawara kan neman belinsu.
An gurfanar da tsohon Gwamnan ne a gaban kuliya bisa sabbin tuhume-tuhume 16 da hukumar EFCC ta gabatar masa.
A halin da ake ciki, kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Yahaya Bello a hukumar EFCC.













































