Wata hukumar kula da fasahar kere-kere, BudgIT ta soki majalisar dokokin kasar kan amincewa da kasafin kudin shekarar 2022 duk da cewa akwai wasu ayyuka guda 460 da aka maimaita a cikin kasafin kudin wanda kudin su ya ya kai Naira biliyan 378.9.
A cikin binciken da ta gudanar, BudgIT ta ce “kashi 64% na kasafin kudin da aka ware domin siyan babura, fitilun tituna da sauran ayyukan da suka sabawa aikin sa. Wannan ba gaskiya ba ne musamman ganin yadda al’ummomin wadannan jihohin ke fama da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda wadanda sukan shigo da babura.”
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun mai kula da harkokin sadarwa na BudgIT, Iyanu Fatoba, a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa “BudgIT, wata kungiya mai zaman kanta ta civic-tech da ke jagorantar fafutukar tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin kudaden gwamnati na Najeriya, ta yi kira ga ‘yan kasa, kungiyoyin farar hula, kamfanoni masu zaman kansu, da kuma kasashen duniya da su gaggauta sanya baki kan wannan batu domin janyo hankalin Majalisar Dokoki ta kasa da Fadar Shugaban kasa cikin gaggawa don gyara da kuma kawar da kura-kurai a cikin kasafin da aka amince da shi na 2022.
“Binciken farko da muka yi kan manyan ayyuka 21,108 a cikin kasafin kudin shekarar 2022 da aka amince da su, ya nuna ayyuka 460 an sanya su fiye da sau daya a cikin kasafin wanda suka kai Naira biliyan 378.9. Ku tuna cewa BudgIT ta lura da ayyukan da aka maimaita guda 316 a cikin kasafin 2021 na FG wanda majalisar kasa ta amince da shi.
“ICPC ta tabbatar da kwafi guda 257, yayin da ofishin kasafin kudi ya tabbatar da cewa akwai wasu ayyuka guda 185 da aka maimaita wanda kudinsu ya kai Naira billiyan 20.13bn, bayan sun sanar da jama’a cewa ba a fitar da kudaden ayyukan a shekarar 2021 ba.
BudgIT ta koka da yadda hauhawar farashin kaya ke durkusar da tattalin arzikin kasar, amma duk da haka ‘yan majalisar tarayya na ci gaba da gudanar da ayyukan cin hanci da rashawa domin kara jefa Najeriya cikin tabarbarewar tattalin arziki.










































