Gwamnatin Ekiti ta yi gargaɗi kan shirin gasar sumbata a jihar

358454412 756443083151503 2598367163539855024 n
358454412 756443083151503 2598367163539855024 n
Gwamnatin jihar Ekiti ta yi kakkausan gargadi ga kungiyar da ke shirin karbar bakuncin sumbata ta tsawon lokaci, wacce a turance a ke kira da kiss-a-thon, ta kwanaki uku a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Isaac Adelusi, a madadin babban sakataren ma’aikatar al’adu da yawon bude ido a Ado-Ekiti.
A cewar gwamnati, gasar ta kiss-a-thon, wacce aka shirya da nufin shiga kundin tarihin duniya na Guinness, zai gudana ne a daya daga cikin wuraren karbar baki a jihar.
“Wannan gasa da aka shirya, ba kawai rashin tarbiyya ba ce kaɗai, shirye ce da rashin kunya da fitsara tare da ɓata sunan jihar. Kuma shiri ne da ya sabawa kimar al’ummarta, don haka zai iya gurɓata tarbiyyar matasan mu .” Inji gwamnatin.

A nan ne ma’aikatar fasaha, al’adu da yawon bude ido ta haramta gudanar da irin wannan gasa ko duk wani abu makamancinsa a duk wata cibiyoyin ma’aikatar a jihar Ekiti.
Don haka ma’aikatar ta yi kira ga ‘ya’yan kungiyar masu otal-otal ta Ekiti, da su sa ido sosai kan gidajen su don kada a yi amfani da su wajen haifar da abin kunya ga gwamnati da al’ummar jihar Ekiti.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here