Lai Mohammed ya samu sabon aiki

lai mohammed new
lai mohammed new

Tsohon ministan yaɗa labaran Najeriya Lai Mohammed ya samu sabon aiki da wani kamfanin ayyukan kamun ƙafa na ƙasa-da ƙasa, na Ballard Partners.

A wani sakon Tuwita da kamfanin ya wallafa ya ce ya naɗa Lai Mohammed a matsayin jami’in gudanarwa.

Sanarwar ta ce kamfanin na Ballard Partners wanda ke ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke kyautata alaƙa tsakanin ɓangarorin gwamnati a Amurka, ya buɗe reshensa na farko a nahiyar Afirka a Abuja babban birnin Najeriya.

Shugaban kamfanin Brian Ballard ya ce kamfanin ya bai wa Lai Mohammed aikin ne kasancewar yana ɗaya daga cikin mutanen da ake ganin kimarsu a Najeriya.

Jaridar Punch ta ambato Lai Mohammed na bayyana jin daɗinsa na kasancewa ɗaya daga cikin ma’aikatan kamfanin Ballard Partners mai kyakkyawan tarihi a ayyukasa a faɗin duniya.

“Na ji dadin fara aiki da kamfanin Ballard Partners tare da buɗe ofishinsa a na farko a Afirka”, in ji Lai Mohammde.

Lai Mohammed dai ya shafe shekara takwas a matsayin ministan yaɗa labarai a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa  Muhammdu Buhari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here