Rundunar ƴansanda a jihar Ogun ta ce ta kama wani mamba mai yi wa kasa hidima, NYSC, Adebola Sodiq, bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 20 fyade (an sakaye suna).
Kakakin rundunar, SP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta a jiya Asabar.
Oyeyemi ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin biyo bayan rahoton da aka kai a hedikwatar Owode Egba da ke karamar hukumar Obafemi Owode a jihar.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, wacce aka yinwa fyaɗen ta bayyana cewa wanda ake zargin saurayi ne a wajen kawarta na kut-da-kut.
“Ta ce ya zo gidanta ne inda take zaune tare da abokan aikinta a ranar 9 ga watan Mayu inda ya bukaci ta bi shi ya saya mata kyauta domin murnar zagayowar ranar haihuwarta.
“Ta bayyana cewa a matsayinta na ƙawar budurwar wanda ake zargin, ba ta da dalilin zargin wani wasa mara kyau tsakanin su, don haka ta bi shi.
“Amma yayin da suke tafiya, wanda ake zargin ya bukaci ta bi shi har harabar makarantar da yake koyarwa ta hidimar kasa, domin dauko jakarsa.
“Da isa harabar makarantar da ke kauyen Agbajege, wanda ake zargin ya ja ta da karfi zuwa dakinsa inda ya sadu da ita ba da don ranta ba duk da magiyar da ta riƙa yi masa,” inji shi.
Oyeyemi ya bayyana cewa da samun rahoton, Bature Ƴansanda, DPO, sashin Owode Egba, Olasunkanmi Popoola, ya bayar da umarnin kama Sodiq.
Ya kara da cewa da ake yi masa tambayoyi ya amsa laifinsa amma ya ce bai san abin da ya same shi ba.
Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa ‘yan sandan sun kai wacce aka yi wa fyaɗen zuwa babban asibitin Owode Egba domin duba lafiyarta.
A halin da ake ciki, kwamishinan ƴan sandan jihar Ogun, Olanrewaju Oladimeji, ya bayar da umarnin a mika Sodiq zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.












































