Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana Allah-Allah ya koma mahaifarsa da ke Daura a jihar Katsina bayan mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin bikin sallarsa na tara kuma na karshe a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban kasar ya ce ya yi matukar sa’a da ya jagoranci kasar Najeriya a mataki daban-daban.
Ya kuma yi godiya ga mutanen Abuja da suka yi hakuri da shi tsawon shekaru bakwai da rabi da suka gabata.
“Ina godiya ga mazauna Abuja da suka yi hakuri da ni tsawon shekaru bakwai da rabi da suka gabata.
“Na matsu na tafi gida. Da gangan na yi tanadin da zan kasance nesa da ku.
“Na samu abun da nake so kuma baki shiru zan yi ritaya zuwa mahaifata a garin Daura.”
“Ina kirga kwaaknin. Damokradiyya abu ne mai kyau idan ba don haka ba ta yaya mutum daga daya bangaren zai zama shugaban kasa na wa’adi biyu?”
Yayin da yake kuma jadadda kusancinsa da kasar Nijar, shugaban kasar ya ce:
“Kilomita 8 ne daga mahaifata (Daura) zuwa kasar Nijar.”
Wannan ba shine karo na farko da shugaban kasar ke cewa ya matsu ya koma mahaifarsa ba domin a watan Yulin bara, ya bayyana cewa ya matsu ya koma gonarsa, wanda iyaye da kakanninsa suka bar masa a Daura.












































