Ƴan sanda sun kama masu satar ƙarafan titin dogo a Ilorin da Kano da Gombe

Rail tricks

Rundunar ‘yan sandan hukumar sifurin jiragen kasa, a jihohin Kwara da Kano da Gombe ta sanar da kama wasu mutane da ake zargi da yin barna a manyan hanyoyin jirgin kasa.

Manajan Daraktan Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya NRC, Dakta Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin a Lagos.

Opeifa ya ce suna zargin bata garin da sace kayayyakin hukumar da suka hadar da manya da kananan karafa da Notika da Takalmin birki da sauransu inda suka kwance su a wasu kebabbun layikan dogo.

“A ranar 11 ga watan Yuni, wani ma’aikacin tashar jirgin kasa da ke Ilorin, Mista Adesina Fabumi, ya kai wa rundunar ‘yan sandan rahoton cewa barayin da ba a san ko su wanene ba sun kwashe farantan tayar jirgi guda 56 da sauran muhimman kayayyaki a tsakanin kilomita 413 zuwa 414 a kusa da kauyen Idi-Ose, a Ilorin.

Shugaban na NRC ya kara da cewa a ranar 18 ga watan Yuni, an kama wani wanda ake zargi Usman Bashir inda aka same shi da kayayyakin layin dogo da yawa a hannun sa.

Ya ce a halin yanzu Sufeta Oniwara Musa, ya na taimakawa wajen gudanar da bincike wanda zai kai ga cafke wadanda ake zargin.

Opeifa ya nanata kudirin kamfanin na kare kayyadaddun kadarorin layin dogo sannan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da aikata barna za a tabbatar da cewa ya gamu da mahukunta.

Shugaban NRC ya ce, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane hudu a ranar 15 ga watan Yuni, biyo bayan wani rahoton barna a layin dogo a garin Zakirai da ke karamar hukumar Gabasawa.

A cewarsa, an gurfanar da mutanen hudu a gaban kotu kuma sun amsa laifin da ake tuhumar su da su, kuma kotu ta yanke musu hukunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here