Zaben 2023: Ya kamata talakawa su yi amfani Da ƴan daba domin hana magudi- Muhammad Bashir

IMG 20211023 WA0008
IMG 20211023 WA0008

By Muhammad Bashir Kano

Abinda ƴan siyasarmu suke na bai wa masu Shaye-shayen cikin mu fa, bai taka kara; ya karya ba, kuɗaɗe ne ƙalilan wadanda idan mutanen gari suka zage, za su iya bayarwa su ma.

Amma saboda ganin girman kyautar da suke musu, ya sa suke hana mu sakat a ko ina musamman a ranakun zaɓe.

Duk mun sani; mun kuma yar da cewa komai taƙadaranci ko fitsarar ɗan daba akwai waɗanda yake girmama wa; yake jin maganar su kuma suna yin haka ne saboda wani abu da suke samu ne a wurin su na kyauta, ko jan su a jiki.

Waɗannan ƴan daba a zahiri talakawa sun fi zama da su fiye da ƴan siyasa; kuma sun fi su sanin halayen su, saboda su ne iyayen su da ƴan uwansu da abokan su; sa’annan kuma a cikin unguwannin su suke dab dalar rayuwarsu.

Ƴan siyasa ba sa neman su sai lokaci zuwa lokaci, wanda idan ya wuce ba za su ƙara neman su ba har sai wata buƙatar ta taso sai su ƙara aiko su cikin al’umma a buge su tayar wa da kowa hankali.

Yanzu babbar matsalar da ta tunkaro mutanen Arewa ita ce ta yawaitar masu shaye-shayen nan, kuma ko mun ƙi, adadin su ƙaruwa yake yi a kullum ba bu yara; ba bu manya; sannan ba bu matan aure; ba bu ƴan mata.

Dangane da batun zaɓe kuwa, da yawan mutane suna zargin cewa lokacin da ƴan daba suke afkawa rumfunan kada ƙuri’a a wurare daban-daban akwai jami’an tsaro a wurin da kuma manyan ƴan koren ƴan takara.

Haka za su ci karensu babu babbaka su ɗauke akwatun zaɓe wani lokacin su sassara ko ma kashe waɗansu su bar wurin ana ji ana gani.

Zargin da mutane suke yiwa ƴan siyasa “Cewa suna yin amfani da ƙarfin ƴan daba da kuma daukar nauyin jami’an tsaro domin ba su kariya” zai iya zama tarihi idan iyaye da ƴan uwa suka tashi tsaye haiƙan suka janyo matasan nan a jikin su to za su tsawatar masu idan sun yi yunƙurin aikata laifi a lokacin zaɓe, kuma za su ji.

Wannan matakin idan aka ɗauke shi, lallai za’a ga sauyi a lamarin maguɗin zabe da ƴan siyasa suke aikatawa, duk da ba zai yiwu a samu nasarar ribatar duk masu saye-shaye ba, amma nan da lokacin zaben 2023 idan mutane sun yi niyya, za su iya cin nasarar kwace matasan nan daga hannun gurɓatattun shugabanni masu yin amfani da yaranmu; suna jefa mu cikin wahalar rayuwa ta shekaru wadda ita ce ke janyo matsalar sace-sace da laifuka a Arewa yanzu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here