‘Yan Sanda sun tsare mata bisa zargin kashe kishiyarta da tabarya a Bauchi

Police badge

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Bauchi ta ce ta kama wata matar aure bisa zargin kashe kishiyarta biyo bayan wani lamarin tashin hankali a gida a Bauchi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Litinin a Bauchi.

Ya ce rundunar ta tsare wacce ake zargi a ranar 27 ga Satumba kan zargin kisan kai da ganganci biyo bayan wani lamari na cikin gida a Rukunin Gidaje na Tafawa Balewa a Bauchi.

Habib ya ce a ranar 27 ga Satumba, da misalin karfe 4:05 na yamma, C-Division na ‘yan sanda a Bauchi, ya samu sahihan bayanai cewa an samu tashin hankali a gida tsakanin mata biyu da ke zaune a gida daya mallakin mijinsu.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wacce ake zargi mai shekaru 33, wacce ita ce amarya, ana zargin ta hari kishiyar cikin yanayin gushewar tunani, inda ta buga wa uwar gidan tabarya a goshi, nan take ta fadi ba tare da sanin inda kanta yake ba.

“Bayyan an karbi rahoton, jami’an bincike da ke karkashin C-Division sun garzaya wurin da lamari ya faru nan take.

“An kammala lamarin, yayin da kuma aka garzaya da wanda aka raunata zuwa Asibitin Kwararru na Bauchi, inda likita ya tabbatar da mutuwarta, aka kuma ajiye gawar a dakin ajiye gawa na asibiti don gudanar da bincike,” in ji shi.

Habib ya ce ‘yan sanda sun karbo tabaryar da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Ya bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda, Sani Omolori Aliyu, ya yi umarnin da a mika lamarin ga Sashen Kula da Manyan Laifuka (SCID) don gudanar da bincike na sirri da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.

Aliyu ya jajanta wa iyalan mamaciyar ya kuma yi gargadi game da tashin hankali a gida.

CP din ya kuma shawarci mazaje da su nemi tallafin likita da na zamantakewa kan lokaci ga iyalansu da ke nuna alamun rashin lafiyar kwakwalwa. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here