Tinubu ya taya Sarki Charles lll murna

Bola Tinubu new new
Bola Tinubu new new

Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya sabon sarkin Ingila Charles III murnar bikin naɗinsa da aka yi yau.

A cikin wata wasiƙar taya murna da Tinubun ya aike wa Sarki Charles lll ya ce a shirye yake domin yin aiki tare da sabon sarkin.

Tinubu ya ce yana da yaƙinin sarkin zai bi sawun mahaifiyarsa Sarauniyar Elizabeth ll, wajen kawo ci gaba a Birtaniya da ƙasashen ƙungiyar rainon Ingila ta Commonwealth.

Zaɓaɓɓen shugaban wanda ke jiran rantsuwar kama aiki, ya ce yana fatan dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya za ta ci gaba da ƙarfafa a tsawon zamanin mulkin Sarki Charles lll.

”A matsayina na zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, ina fatan cewa a zamanin mulkinka, za a samu yauƙaƙar dangantaka tsakanin Najeriya da Birtaniya domin ciyar da ƙasashenmu gaba”, in ji Tinubu.

Daga ƙarshe Tinubu ya yi addu’ar samun ƙwarin gwiwwa tare da nasara ga sabon sarkin a ilahirin tsawon mulkisa.

A ranar 29 ga wannan wata ne dai za a rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya bayan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan Fabrairu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here