Shugaban jam’iyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa na Dan majalisar Dattawa Mai wakiltar Nasarawa ta Arewa.
Sanata Adamu ya aikewa majalisar wasikar sauka daga mukaminsa ne bayan zabarsa da aka yi a matsayin Shugaban jam’iyyar APC na Najeriya a Ranar 26 ga watan Maris din shekarar 2022.
Yace matakin da ya dauka na barin majalisar ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilun da muke ciki.
Shugaban majalisar Dattawa Dakta Ahmad Ibrahim Lawal shi ne ya karanto matakin da Shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya dauka a zaman majalisar na Ranar Talata.
A cikin wasikar tasa ya yabawa shugabancin majalisar karkashin jagorancin Sanata Ahmad Lawal.
“Ya zame min dole na yaba da salon jagorancinka mai cike da kwarjini da adalci ta yadda kake bawa ko wanne Sanata damarsa ba tare da nuna bambancin Jam’iyya ba.” Inji Sanata Adamu.
Kafin yayi murabus daga kujerar Dan majalisar Dattawan, Abdullahi Adamu ya rike mukamin gwamnan jihar ta Nasarawa har wa’adi biyu daga shekarar 1999 zuwa 2007 sannan Kuma yaci gaba da zama a majalisar Dattawa har karo uku.












































