Masu Gonaki da Filaye sun gudanar da Sallar Al’ƙunuti kan yunƙurin gwamnati na sake kwace musu kadarori don gina sabuwar kasuwa

WhatsApp Image 2025 11 08 at 15.00.11 540x430

Mazauna unguwar Dangoro da ke cikin ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun gudanar da Sallar Al’ƙunuti da addu’o’i na musamman a ranar Asabar, suna neman taimakon Allah kan abin da suka kira ci gaba da kwace gonaki da filayensu da gwamnati ke yi.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mazauna yankin sun bayyana damuwarsu bayan samun labarin cewa gwamnatin jihar na shirin mayar da kasuwar ’Yan Lemo da ta ’Yankaba zuwa yankinsu, abin da suke tsoron zai sake haifar da kwace ƙasa da korar mutane daga gidajensu.

Wani daga cikin masu fili a yankin Sadik Muhammad Abdullahi, ya bayyana takaici kan yadda suke ta rasa kadarorinsu saboda ayyukan gwamnati, inda ya ce wannan ne karo na huɗu da hakan ke faruwa a Dangoro.

Ya ƙara da cewa a baya gwamnati ta kwace masa gonaki takwas amma ta ba shi ƙasa ɗaya da rabi a matsayin diyya, sannan yanzu filin da ya sake siya shi ma ana son kwacewa.

Abdullahi ya ce idan aka aiwatar da wannan sabon shiri, mutane da dama za su yi asara, domin filayen a yankin na hannun mutane ne daban-daban, kuma hakan zai wahalar da su wajen samun diyya ta gaskiya.

Ya ce wannan matsalar na iya jawo tashin hankali da asarar rayuka saboda tsananin damuwa da ake ciki.

Wani mazaunin yankin, Nuraini Adabayo, ya ce al’umma sun shiga tashin hankali tun bayan jin wannan shirin, inda ya bayyana cewa shi ya rinƙa karfafa wa wasu gwiwa su sayi ƙasa a yankin, amma yanzu duk sun shiga cikin rashin tabbas saboda yuwuwar kwace filayensu.

Ya kuma ce gwamnati ta ba su gajeren lokaci, inda ake sa ran a fara tantance filayen domin diyya a ranar Litinin.

Ya yi kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sake tunani kan shirin tare da duba yiwuwar mayar da kasuwannin zuwa Cibiyar Tattalin Arzikin Kano, inda ya ce akwai isasshen fili da zai iya ɗaukar ’yan kasuwa ba tare da kwace ƙasa daga mutane ba.

Wani wakilin al’umma, mai suna Alhaji Gambo Saminu Adamu ya kuma bukaci gwamnati ta gaggauta magance matsalar domin guje wa abin da ya kira barazanar rikici da wahala ga jama’a.

Ya roƙi gwamnan da ya kai ziyara a yankin domin ganin halin da suke ciki da idonsa.

Sai dai dagacin Dangoro, Ishaq Yusuf Ishaq, ya ce ba zai yi sharhi ba saboda batun bai fito daga ofishinsa ba, yayin da daraktan wayar da kai na ma’aikatar ƙasa ta jihar Kano, Murtala Shehu Umar, ya ce bai da masaniya game da wannan shiri.

Mazauna yankin sun ce za su ci gaba da roƙon taimakon Allah tare da kira ga gwamnati da ta dakatar da shirin, domin kauce wa abin da suka bayyana a matsayin barazana ga rayuwarsu da gadon kakanninsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here