Aƙalla mutum 19 sun mutu a wani haɗarin mota bayan da gada mai rauni ta rushe a kauyen Fass, ƙaramar hukumar Gumi ta jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar, kimanin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da mota ɗauke da baƙin biki ta faɗo daga gadar da ta rufta cikin ruwa, inda maza, mata da yara suka rasu.
Wani mazaunin yankin, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ‘yan uwa a cikin haɗarin, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a lokacin da ake raka kanwar sa zuwa gidan mijinta a Jega.
Mahaifin amaryar, marigayi Sheikh Dauda Fass, tsohon ɗan majalisar dokokin jihar ne.
An ce za a binne mamatan washegari da safe.
Gadar da ta haɗa al’ummomi da dama ciki har da Gwalli, Yar Gusau da Fass, ta daɗe tana a alace.
An fara gyara ta ne a zamanin tsohon gwamna Abdulaziz Yari, amma ruwan sama mai yawa ya sake lalata ta kimanin shekaru bakwai da suka gabata, lamarin da ya bar mazauna yankin cikin wahala wajen yin zirga-zirga.
A farkon shekarar nan, al’umma sun yi ƙoƙarin cike wuraren da suka lalace da yashi ta hanyar haɗin gwiwa, amma daga ƙarshe gadar ta rushe gaba ɗaya, abin da ya haddasa wannan mummunan lamari.
Babangida ya dora alhakin lamarin kan sakacin gwamnati da kin kula da gada, yana mai cewa, “Tun wancan lokaci muke wahala.
Wasu lokuta sai sun shiga cikin ruwa don zuwa makabarta mu binne mamaci.
“Har ma mun cike buhunan shinkafa da siminti da yashi don gina wata ƙaramar gada ta wucin gadi.”
Mazauna yankin da suka yi magana sun koka kan yadda lalacewar gadar ke kawo cikas ga rayuwarsu, musamman a lokacin damina. Wasu sun bayyana tsoron kada ruwa ya tafi da su idan suka yi ƙoƙarin tsallaka.
Sun bayyana wannan lamari a matsayin wani sabon ƙarin ƙalubale a cikin “rayuwar firgici” da suke fuskanta a Zamfara, inda suka soki ikirarin gwamnati na magance muhimman ayyukan raya ƙauyuka.
Da aka tuntubi mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal, Mustapha Jafaru Kaura, ya ce bai san da wannan al’umma ko lamarin ba, amma ya yi alƙawarin tuntuɓar hukumomi. Sai dai daga bisani bai ƙara amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
Al’ummar yankin sun roƙi gwamnati ta tarayya da ta jiha da su gaggauta gina sabon gada don kare rayuka, tare da gargadin cewa ba za su yarda da “alkawura na bogi” ba.













































