Gwamnatin jihar Adamawa ta dawo wa da ma’aikata 1,699 aikin su, bayan gwamnatin da ta gabata ta kore su

Governor of Adamawa State Ahmadu Fintiri
Governor of Adamawa State Ahmadu Fintiri

Gwamnatin jihar adamawa ta ce ta dawo wa da ma’aikata 1,699 aikin su, bayan da gwamnatin da wuci ta kure su.

Babban daraktan yada labarai na gwamna Ahmadu Fintiri, Solomon Kumangar ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN hakan a yola ranar Litinin.

Ya ce wadanda abin ya shafa sune malaman makaranta 699 na rukunin D, wadan da gwamnatin da wuce ta dauka sanan ta tura su makarantu sakandare da kuma Firamare suma an dawo musu da aikin su.

Ya kara da cewa tun da farko ma’aikatan lafiya 1,000 gwamnatin ta dawo musu da aikin su, bayan gwamnatin da wuci suma ta kore su ba bisa ka’ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaitu cewa gwamnatin ta Adamawa ta dauki ma’aikatan lafiya 1,113 a jihar, sanan ta kuma tura su kauyukan jihar don kara inganta harkokin lafiya a kauyukan.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here