Gwamnatin Jihar Filato ta ba da umurnin rufe duk wata makarantar firamare da sakandare ta gwamnati da ta masu zaman kansu na dan lokaci sakamakon barnar da cutar mashako ke yi.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne domin kare dalibai daga kamuwa da cutar.
Wannan rufewar na zuwa ne kwanaki kadan bayan jami’an lafiya sun tabbatar da mutuwar wasu mazauna yankin Jos ta Arewa sakamakon matsalolin da ake zargin ta cutar mashako ce.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr Nicholas Baamlong, ya bayyana a ranar Talata cewa kimanin mutane 23 ne suka mutu sanadiyyar cutar, yana mai cewa gwamnatin jihar ta tsananta matakan shawo kan yaduwar wannan cuta mai saurin yaduwa.
Baamlong ya ce an kwantar da marasa lafiya tara a Babban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos da kuma Asibitin Kwararru na Jihar Filato.
A cikin wata sanarwa da Kwamishiniyar Yada Labarai da Sadarwa, Rt. Hon. Joyce Lohya Ramnap ta sanya wa hannu a ranar Asabar, gwamnatin ta ce umurnin zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 7 ga Satumba 2026, kuma zai ci gaba da aiki har sai yadda hali ya yi.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa Gwamna Caleb Manaseh Mutfwang ya ba da umurnin ne biyo bayan rahotannin zargin bullar cutar mashako a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Wase, Jos ta Kudu da Bassa.
Gwamnatin ta ce makarantun da suka riga suka koma karatu su ma dole ne su rufe daga ranar Litinin, an yi kira ga masu makarantu, masu gudanarwa, malamai, iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da cewa dalibai sun zauna a gida tsawon wannan lokacin domin kare lafiyar da rayuwarsu.
“Gwamnati na godiya ga fahimta da cikakken hadin kai na dukkan masu ruwa da tsaki yayin da ake ci gaba da daukar matakan da suka dace don amfanin al’ummar Jihar Filato,” in ji kwamishiniyar.













































