IGP ya nada DCP Anthony Placid a matsayin sabon jami’in hulda da jama’a na rundunar, don ya maye gurbin Hundeyin

DCP Anthony Placid police 720x430

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya amince da nadin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP), Anthony Placid, a matsayin sabon Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (FPRO).

Placid zai maye gurbin tsohon jami’in hulda da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Hundeyin ya fitar a ranar Lahadi daga hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa Placid ƙwararren jami’in ‘yan sanda ne da ke da gogewa sosai a fannoni da suka haɗa da mulki da gudanarwa, ayyuka, tattara bayanan sirri, horaswa da kuma ayyukan wanzar da zaman lafiya na ƙasa da ƙasa.

An haifi Placid a Uyo na jihar Akwa Ibom, kuma ya fito ne daga Mbiokporo Nsit a ƙaramar hukumar Nsit Ibom ta jihar.

Yana da digirin farko na Kimiyya a fannin ilimin ƙasa da tsara yankuna daga Jami’ar Uyo, sannan yana da digirin digirgir a fannin doka da diflomasiyya daga Jami’ar Jos.

Haka kuma ya karanci shari’a a Jami’ar Bude ta Kasa ta Najeriya, inda ya samu digirin LLB.

An ɗauke shi aiki a rundunar ‘yan sanda a matsayin Cadet ASP a Kwalejin ‘Yan Sanda ta Najeriya da ke Kano a shekarar 1996, sannan aka ba shi mukamin jami’i a Agusta 1998.

Ya halarci kwasa-kwasai na ƙwarewa da dama na cikin gida da na ƙasa da ƙasa, ciki har da horon ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya samu takardun shaidar ƙwarewa a fannoni kamar nazarin ‘yan sanda, nazarin soji, wayar da kan jinsi, dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa, haƙƙin bil’adama da kare fararen hula.

Haka kuma ya halarci kwas na manyan shugabanni da gina zaman lafiya na UNITAR a ƙasar Kenya.

Placid ya yi aiki a mukamai daban-daban masu muhimmanci a cikin gida da wajen ƙasar, ciki har da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Adamawa, PPRO a Kwalejin Horas da ‘Yan Sanda ta Jos, babban jami’in horaswa a Ofishin Tarayyar Afirka a Sudan, da kuma shugaban horaswa da ci gaba a Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Darfur.

Haka kuma ya taba zama DPO a rukunin gidan tarayya da ke Calabar, Bakassi, Uruan da Gembu, jami’in kula da sashen yaki da fashi da makami a Kaduna, mashawarcin tsaron zabe na Tarayyar Afirka, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na ayyuka a Akwa Ibom da Kogi, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na sashen bayanan sirri a Abia, da kuma mataimaki mai kula da harkokin gudanarwa da kudi a hedikwatar shiyya ta 3 da ke Yola.

Placid mamba ne na Kungiyar Shugabannin ‘Yan Sanda ta Duniya, sannan kuma mai horaswa kan haƙƙin bil’adama na Commonwealth, da kuma mai horaswa ga Kwamitin Agaji ya Red Cross na Duniya a fannin dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa.

Shi ma ya kammala Babban Kwas na Gudanar da Manufofi da Dabarun Kasa karo na 47 a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Kasa (NIPSS) da ke Kuru, inda aka karrama shi da memba na cibiyar (mni) kafin daga bisani a mayar da shi aiki a jihar Cross River.

Placid yana da mata da yara, kuma yana sha’awar sauraron kiɗa da kuma wasannin ƙwallon ƙafa, ƙwallon kwando, tebur tennis da badminton.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here