NDLEA ta kaddamar da shirin ‘Operation Ramadan Mubarak’, ta kama mutane 13 a Kano

NDLEA 1

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta ƙasa reshen jihar Kano ta kaddamar da shirin “Operation Ramadan Mubarak”.

Aikin wata manufa ce ta musamman da aka tsara domin tarwatsa hanyoyin safarar miyagun kwayoyi kafin watan azumin Ramadan.

Wannan na cikin sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar ranar Juma’a a Kano.

Ya ce aikin, karkashin jagorancin Kwamandan Jihar, Dahiru Yahaya-Lawal, zai karfafa wuraren bincike, rushe maboyar masu sayar da kwayoyi a cikin birnin Kano da kewaye, tare da dakile shigowar miyagun kwayoyi cikin jihar.

Ya ce yayin kaddamar da aikin ranar Alhamis, jami’ai sun kai samame a yankin Kofar Mata, kauyen Danzaki, Fagge, Kofar Wambai da yankin Rimi.

Samamen ya kai ga kama mutane 13 ciki har da mata biyu, tare da kwato miyagun kwayoyi daban-daban da suka hada da cannabis sativa, diazepam, “suck and die” da rubber solution.

Yahaya-Lawal ya ce aikin na nuna kudurin rundunar na hana masu safarar miyagun kwayoyi amfani da watan Ramadan wajen yada su.

Ya nuna damuwa cewa wasu bata-gari kan yi amfani da watan Ramadan wajen gudanar da Safarar kwayar, yana mai cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi kan haddasa aikata laifuka masu tayar da hankali.

Yahaya-Lawal ya kara da cewa bisa umarnin Shugaban NDLEA, ritaya Birgediya Janar Mohamed Buba-Marwa, hukumar za ta kara zage damtse wajen sintiri, karfafa wuraren bincike da ci gaba da aiki bisa bayanan sirri domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Ya bukaci jama’a su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani abin zargi ko bayanai kan safarar miyagun kwayoyi ga ofishin NDLEA mafi kusa ko ta hanyoyin sadarwa na hukuma.

Ya ce hadin kan al’umma yana da matukar muhimmanci wajen kare lafiyar jama’a, gudanar da ibadu da walwalar mazauna jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here