Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taya Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari, murnar cikarsa shekaru 30 a kan karagar mulki, inda ya bayyana shi a matsayin jagora mai hangen nesa da jajircewa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a Abuja, Tinubu ya yaba da jajircewar Sarkin wajen tabbatar da zaman lafiya, adalci da ci gaban garin Ilorin da kewayenta.
Shugaban ƙasan ya gode wa mai martaba bisa irin jagorancin da yake bayarwa wanda ya tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa a jihar Kwara.
Ya bayyana Sarkin Ilorin, Alhaji Sulu-Gambari, a matsayin mutum mai mutunci da kima, wanda ya yi wa ƙasa hidima kafin hawansa karagar mulki, kuma yanzu yana ci gaba da hidima a matsayin shugaba a jami’ar Bayero ta Kano.
Tinubu ya kuma jaddada cewa aikin Sarkin a fannin shari’a, musamman a matsayin alkalin kotun daukaka ƙara, ya kasance abin koyi wajen rikon gaskiya da adalci ba tare da tsoro ko son rai ba.
Shugaban kasar ya roƙi Allah ya ƙara wa Sarkin lafiya da tsawon rai mai albarka domin ci gaba da jagoranci mai amfani ga al’umma.












































