Hukumar kula da ƴan sanda ta amince da naɗin Dankwara Mohammed a matsayin Mataimakin Sufeton ‘Yan sanda (DIG) domin wakiltar yankin Arewa maso Gabas.
Naɗin ya biyo bayan ritayar tsohon mai rike da mukamin, Sahabu Yahaya.
Shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a a birnin Abuja, inda ya ce Mohammed kafin haka yana rike da mukamin Babban Sufeto na ‘Yan sanda (AIG).
Hukumar ta kuma amince da ɗaga mukamin Abibo Reuben daga kwamishinan ‘yan sanda zuwa babban sufeto na ‘yan sanda, tare da ƙarin ɗaukaka wasu mataimakan kwamishinoni 11 zuwa matsayin kwamishinoni.
Daga cikin sabbin kwamishinonin akwai Naziru Kankarofi, Nendel Gomwalk, Tijani Fatai, Wilson Akpan, Morkwap Dongshal, Abdullateef Yusuf, Cletus Nwadiogbu, Ahmed Bello, Abdulraheem Nurudeen, Patrick Daaor da Umar Hadejia.
Bugu da ƙari, hukumar ta amince da ɗaukaka mataimakan kwamishinoni 15 zuwa mukamin mataimakin kwamishina (DCP), ciki har da David Ojo, Umaru Bichi, Bala Jarumai, Makanjuola Abiodun, Shafii Abdulkarim, Mohammed Ajose, Mukter Bello, Mada Adamu, Omololu Vaughan, Linus Ogbodo, Emmanuel Ogbuanya, Tijani Gotom, Shehu Ibrahim, Onwuegbuzie Awele, da Hamza Ali.
Haka kuma, an ɗaga jami’ai 44 daga matsayin babban sufeton ‘yan sanda (CSP) zuwa mataimakin kwamishina (ACP), yayin da jami’ai 412 suka samu ɗaukaka zuwa CSP daga SP.
Shugaban hukumar, Hashimu Argungu, ya taya sabbin jami’an da aka ɗaga murna tare da kira gare su da su ƙara sadaukar da kai wajen hidima ga ƙasa.
NAN











































