Gurasa, wani irin burodi zagaye da siriri, wanda asalinsa ya samo tushe a Kano, ya fara ne a matsayin abincin sarakuna da attajirai, amma yanzu ya koma ɗaya daga cikin abinci mafi rahusa kuma mafi shahara a cikin jama’ar jihar da ma Arewa baki ɗaya.
An ruwaito cewa Gurasa ta shigo Kano ne tun ƙarni da yawa daga wajen ’yan tafiye-tafiye na Larabawa, musamman daga Sudan da Aljeriya, waɗanda suka zauna a unguwar Dala.
A wancan lokaci, sarakuna da manyan gidaje ne kawai ke cin sa, amma daga baya talakawa suka rungume shi saboda rahusa da kuma sauƙin sarrafawa.
A yau, Gurasa ba wai kawai abin ci bane, har ma kasuwanci ne da ke ciyar da dubban iyalai a Kano.
A unguwanni irin su Jakara, Chediyar Yan Gurasa da Karofin Dala, kusan duk gida na da hannu a harkar yin Gurasa, kafin ta bazu zuwa Tudun Makera, Aikawa da Rijiya Biyu. Ana cin ta a nau’o’i daban-daban, ciki har da bandashe – Gurasa da ake haɗawa da kuli-kuli, mai da kayan lambu – ko kuma tare da miya da shayi.
Wasu mazauna Kano sun bayyana yadda Gurasa ta zama ginshiƙi a gidajensu. Abubakar Umar ya ce ’ya’yansa kan yi murna idan ya sayo musu Gurasa, saboda ɗanɗano da kuma yadda take sauƙin haɗawa da abinci daban-daban.
Karin labari: Ƴan kasuwa a Kano na ƙera babura masu lantarki, suna haskaka baiwar Najeriya
Haka kuma, Fatima Abubakar ta ce Gurasa na ba ta damar yin karin kumallo, abincin rana ko dare cikin sauƙi.
Kasuwancin Gurasa ya kuma zama gadon iyali a wasu wurare.
Muktar Namaka ya bayyana yadda mahaifiyarsa ta gada daga kakarta, sannan suka ci gaba da rayuwa da shi.
Ya ce har yanzu suna sayarwa a Kano da wasu jihohi, kuma ana gayyatar su domin yin Gurasa a bukukuwa da taruka.
Ana yin Gurasa daga fulawa, yisti, baking powder da ruwa, sannan a jika, a bar shi ya tashi kafin a yi masa siffar zagaye a soya shi a cikin tanderu – wani tandun burmini da ke ba ta ɗanɗano na musamman.
Akwai nau’i biyu: na al’ada wanda ba a haɗa shi da kayan ƙamshi ba, da kuma na musamman da ake ƙara masa kayan miya da ƙanshi, wanda ake siyarwa a lokutan biki.
A halin yanzu, Gurasa tana da darajar fiye da abinci kawai. Ta koma al’ada, sana’a da kuma alamar ɗaurewar al’umma, abin da ya sa ta zama wani ginshiƙi na gadon al’adu da kasuwancin Kano.












































