Martanin gwamnati kan samun allurar rigakafin Corona wanda wa’adinsu ya kare

WhatsApp Image 2021 12 08 at 2.48.54 PM
WhatsApp Image 2021 12 08 at 2.48.54 PM

Rohoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa akalla allurar rigakafin Corona guda Miliyan daya ne wa’adin su ya kare ba tare a da an yi amfani dasu ba a Nigeria tun a watan Nuwamba.

Majiyar Reauters ta ruwaito cewa wannan na daga cikin babbar asarar allurar da aka yi, wanda hakan ke nuna irin wahalar da kasashen Afrika ke sha domin shawo kan cutar.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da wasu daga cikin kasashen Afrika ke neman aka adadin allurar da aka basu.

Sai da gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan wannan rahoton, inda ta bayyana cewa akwai allurar wadda take da karancin wa’adi wanda abu ne mai wuya ta iya kaiwa ga mutane ba tare da wa’adin ta yak are ba.

Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire ya bayyana cewa Nigeria tayi amfani da allurar mai karancin wa’adi sama guda milliyan goma kafin ta lalace, wanda hakan ya bawa gwamnatin damar samun rarar kudi da suka kai billiyan sha shida da digo hudu.

Ministan ya kuma bayyana dalilin da ya sanya Nigeria ta karbin allurar mai karacin wa’adi yana mai cewa saboda yawan al’umma da kasar take dasu da kuma saukin samu wanda hakan zai taimakawa Nigeria wajen rage kasha kudi.

Ya kuma tabbatar da cewa tuni hukumar NAFDAC ta kona allurar wanda ta riga ta lalace

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here