Akalla mahajjatan kasar Pakistan takwas dasuke aikin Umrah ƴan ƙasar Pakistan sun mutu, yayin da shida suka jikkata a wata gobara da ta tashi a wani otal da ke birnin Makkah.
Da yake maida jawabi ga manema labarai game da asarar rayuka a gobarar otal din Makkah, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya ce, “muna da rahoton mutuwar ‘yan Pakistan takwas, shida kuma suka jikkata.
Domin basu agajin gaggaws ga wadanda abin ya shafa da iyalansu, Ofishin Jakadancin mu na Jeddah na tuntubar hukumomin yankin.
Rahotannin farko sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a hawa na uku na otal din dake kan Ibrahim Khalil Road.
Wata majiya ta rawaito cewa alhazan kasar Pakistan, Bangladesh, da sauran alhazan Umrah tuni suka fice daga otal din.
Domin samun sauran shirye shiryen mu latsa nan????????
https://chat.whatsapp.com/HQU1Jxlop03HaIwUpwXc5A












































