Tinubu Bai Bukatar Samun Kaso 25% a Abuja Kafin Lashe Zabe – INEC

INEC Yakubu
INEC Yakubu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shaida wa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa cewa, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin wanda ya yi nasara ba tare da bukatar samun kashi 25 na kuri’un da aka kada a Babban Birnin Tarayya ba.

INEC ta bayyana haka ne a martanin da lauyanta, Abubakar Mahmoud, ya bayar kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar suka shigar a gaban kotun.

Farfesa Mahmoud Yakubu ya ce dan takarar jam’iyyar APC ya cika dukkan sharuddan da doka ta tanada domin a sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, yana mai cewa ba dole ne dan takara ya samu kuri’u kashi 25 cikin 100 a babban birnin tarayya Abuja ba domin a sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba.

“Kunga ba a bai wa babban birnin tarayya wani matsayi na musamman. a cikin kundin tsarin mulki kamar yadda wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar da suka fadi zabe suka bayyana “kuskure”.

Akan dalilin da ya sa aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben, INEC ta ce dan takarar APC ya samu kashi 25 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada a jihohi 29 na tarayya.

“Bayan samun akalla kashi daya bisa hudu na sahihin kuri’un da aka kada a jihohi 29, wanda ya wuce matakin jihohi 2/3 da tsarin mulki ya tanada, baya ga samun mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben.

“Wanda ake kara na farko ya musanta cewa samun kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a babban birnin tarayya, sharadi ne na mutum yasami kaso 25 kafin ayyana shi wanda ya lashe zaben shugaban kasa,” in ji ta.

INEC ta kara da cewa ta bangaren shugabanci, ba ta yi gaggawar daukar mataki ba, kamar yadda Mista Abubakar da PDP suka yi ikirarin cewa Mista Tinubu ne ya lashe zaben.

Ya jaddada cewa Mista Tinubu ya samu kashi 25 cikin 100 na sahihin kuri’un da aka kada a jihohi 29 na tarayya.

Yayin datake zargin Mista Abubakar da jam’iyyarsa game da matsayin babban birnin tarayya Abuja, INEC ta yi korafin cewa “ tanade-tanaden kundin tsarin mulki ya shafi birnin tarayya kamar tana daya daga cikin jihohin tarayya.”

Atiku daganan ta yi iƙirarin cewa bisa ga tanadin tsarin mulki, Abuja “tana da matsayin jiha kuma ya kamata a gane shi kamar jiha ce ta tarayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here