Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshen jami’ar Jos ta bayyana dalilan da suka sa take shirin tsunduma cikin yajin aiki.
Taron, wanda aka gudanar a ranar Juma’a a birnin Jos, an shirya shi ne ta kwamitin hulɗa da ɗalibai na ƙungiyar.
Shugabar ƙungiyar, Farfesa Jurbe Molwus, ta bayyana cewa taron ya ba ASUU damar bayyana matsayinta ga ɗalibai da kuma jan hankalin mahukunta kan halin da ake ciki.
Ta ce manufar taron ita ce sanar da muhimman matsalolin da suka shafi rashin cikakken kulawar gwamnatin tarayya ga buƙatun ƙungiyar.
Farfesa Molwus ta ce ƙungiyar ba za ta iya tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a jami’o’i ba idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da yin watsi da yarjejeniyoyin da aka cimma.
Labari mai alaƙa: Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya ta fara matakin ƙarshe na tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU
Ta ce bayan kwanaki 14 na wa’adin da suka bai wa gwamnati, wanda zai ƙare ranar 13 ga Oktoba, idan ba a dauki mataki ba, za su shiga yajin gargadi na makonni biyu.
Ta bayyana cewa an yanke shawarar wannan mataki ne bayan taron majalisar zartarwa ta ƙasa ta ASUU da aka gudanar a Abuja ranar 28 ga Satumba.
Farfesa Molwus ta ƙara da cewa buƙatun ƙungiyar ba na son rai ba ne, sai dai na neman inganta tsarin ilimi a jami’o’in ƙasar.
A cikin buƙatun ASUU akwai sakin kuɗin farfaɗo da jami’o’i kamar yadda aka tsara a kasafin kuɗi, sanya hannu da aiwatar da yarjejeniyar 2009, biyan haƙƙoƙin ƙarin girma da kuma dawo da mambobin da aka hukunta a wasu jami’o’i na tarayya da na jihohi.
Haka kuma suna neman biyan kaso 23 cikin 35 na ƙarin albashi da kuma biyan watanni uku na albashin da aka dakatar da su.
Shugabar ƙungiyar ɗalibai ta jami’ar, Miss Jane Pwajok, ta yabawa ASUU bisa kiran taron, inda ta bayyana cewa ya ba ɗalibai damar fahimtar ainihin matsalolin dake tsakanin ƙungiyar da gwamnati.
Ta kuma roƙi ASUU da ta duba wasu hanyoyin daban na neman hakkinta maimakon yajin aiki.
NAN













































