Shi kuma dan takarar Sanata na APC Abdullahi Muhammad Sani ya samu kuri’a 182,035.
Kazalika, sakamakon ya nuna dan takarar NNPP Umar Ahmad Tijjani ya samu kuri’a 24,395.
Dan takarar LP kuma, Ibrahim Muhammad Sani ya samu kuri’u 8,7510.
Da wannan sakamakon, yanzu jam’iyar PDP ce ta lashe dukkan kujerun Sanatoci uku da ke a Jihar.











































