Neja: Ɗalibai sun gudanar da zanga-zanga saboda kisan abokinsu

IMG 20250623 WA0029

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja, ta tabbatar da rahoton hallaka wani ɗalibi da bata gari suka yi wanda ya janyo wasu dalibai suka gudanar da zanga-zanga.

A cewar rundunar da misalin karfe 3:00 na dare, ta samu rahoton da ke cewa da misalin karfe 2:30 na dare wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani gidan kwanan dalibai da ke unguwar Ndakitabu ta da ke garin Lapai.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, SP Wasiu Abiodun, ya fitar yau Litinin a Minna babban birnin jihar.

A cewarsa, a nan take jami’an ‘yan sanda daga ofishin garin na Lapai suka garzaya wurin, sai dai wadanda ake zargin ‘yan fashin ne suka tsere.

Ya kara da cewa, “Abin takaici, wani matashi Abdulwahab Abubakar, wanda dalibin digiri ne a matakin aji uku wayau 300 na ilimin kimiyyar sinadarai a jami’ar IBB Lapai, an caka masa wuka a wuyansa, inda aka garzaya da shi babban asibitin Lapai, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

Ya kuma kara da cewa, an fara gudanar da bincike kan lamarin inda kwamishinan yan sandan jihar Adamu Elleman, ya bayar da umarnin a kama wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Daliban da suka gudanar da zanga-zangar sun bayyana lamarin a matsayin rashin daukar matakan kare su daga mahukuntan jami’ar da sauran hukumomi.

Sun ce, ana ci gaba da kai hare-hare kan dalibai tun watanni shida da suka gabata.

A nasa martanin, jami’in hulda da jama’a na jami’ar ta IBB da ke Lapai Baba Mohammed-Akote, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya tabbatar da cewa hukumomin jami’ar na yin duk mai yiwuwa don dawo da zaman lafiya a jami’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here