NAFDAC ta lalata Ƙwayoyin Tramadol guda 491,000 a Kano

Tramadol 750x430

Hukumar kula da harkokin abinci da magunguna ta kasar nan NAFDAC, ta lalata kimanin kwayoyin Tramadol guda 491,000 da suka cafke a nan Kano domin kara bunkasa fannin lafiya.

Darakta bincike da tabbatar da nagartar aiki na hukumar ta NAFDAC Dakta Martins Iluyomade, NAFDAC, ne ya jagoranci lalata kayan a madadin Darakta Janar ta hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye.

Da ya ke ganawa da manema labarai, Adeyeye ya ce, jami’an hukumar hana Fasa Kwauri NCS shiyyar Kano da Jigawa ne suka cafke miyagun kwayoyin bayan da aka yo fasa kyaurinsu zuwa cikin kasar nan.

Dakta Martins Iluyomade, ya ce, a ranar 28 ga watan Mayun bana ne jami’an hukumar da hana da Fasa Kwauri ta kasa, karkashin jagorancin kwanturolan hukumar mai lura da jihohin Kano da Jigawa Dalhatu Abubakar, ne suka samu nasarar cafke kwayoyin.

Ya ce: “Kimar kudin kwayoyin ta kai Naira miliyan 91, kuma wannan aiki ya nuna kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin hukumomin da nufin dakile matsalar fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya.”

Ya kara da cewa hukumar ta jajirce wajen ganin ta kare lafiyar ‘yan Najeriya, sannan ta bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani shakku kan ayyukan miyagun kwayoyi ga hukumar ta NAFDAC domin daukar mataki cikin gaggawa.

Shugaban hukumar ta NCS mai kula da jihohin Kano da Jigawa Dalhatu Abubakar, wanda ya samu wakilcin Yusuf Idris, mataimakin kwanturola, ya ce, an kama kwayoyin Tramadol din ne a kan iyakar Mai Gatari a lokacin aka shigo da su daga Jamhuriyar Nijar.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here