Har yanzu ana kan aikin nazartar jerin waɗanda Tinubu ya yiwa afuwa, kuma za a iya canzawa – Gwamnatin tarayya

Bola Tinubu Tinubu aaaaaaaaaaa 700x430

Ofishin Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a ta bayyana cewa har yanzu ba a saki wani ɗan gidan yari da ya rabauta da yafiyar shugaban ƙasa ba, domin aikin na cikin matakin ƙarshe na duba ingancin jerin sunayen da aka gabatar.

Bayanin hakan ya biyo bayan suka da ce-ce-ku-ce da ke biyo bayan aiwatar da ikon yafiya na musamman da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ga wasu rukuni na fursunoni.

A cewar ma’aikatar, matakin yanzu shi ne na bincike da tabbatar da cewa dukkan sunaye da shawarwarin da aka bayar sun bi ƙa’idar doka da tsari kafin a fitar da takardar saki daga gidan yari.

A wata sanarwa da Alhaji Lateef Fagbemi (SAN), Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, ya sanya hannu a kai, ya bayyana cewa bayan Majalisar Koli ta Ƙasa  ta amince da jerin mutanen da za su amfana, ana buƙatar a ƙarshe ta duba jerin domin tabbatar da daidaituwa kafin a mikawa Shugaban Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa domin aiwatarwa.

Ya ce wannan tsari na tabbatarwa wani ɓangare ne na bin ƙa’idar da ke nuna gaskiya, tare da tabbatar da cewa babu wanda ba shi da cancanta da zai amfana da wannan yafiya.

Fagbemi ya jaddada cewa babu wani jinkiri a cikin aikin, illa dai bin dokar yadda ya kamata domin tabbatar da adalci da gaskiya.

Ya kuma ce da zarar an kammala binciken doka da na tsari, jama’a za su samu cikakken bayani daga gwamnati.

Tun da farko, Majalisar Koli ta Ƙasa ta amince da jerin yin afuwa ga fursunoni, ciki har da waɗanda suka mutu, waɗanda suka kammala zaman kurkuku, da waɗanda ke kan layin kisa da shugaban ƙasa ya gabatar a matsayin masu amfana da ikon yafiyarsa.

Sai dai wannan mataki ya haifar da suka daga jama’a, musamman bayan bayyana cewa an haɗa a cikin jerin wasu da aka yanke wa hukuncin kisa da laifukan miyagun ƙwayoyi, ciki har da Maryam Sanda, wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa bisa laifin kashe mijinta.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here