Gwamnatin tarayya ta raba sama da Naira biliyan 107 ga masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i su 900,000

MSME 750x430

Gwamnatin tarayya ta raba sama da Naira biliyan 107 ga mutane 900,000 a fadin shiyyoyin siyasar Najeriya shida.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa an raba kudaden ne a karkashin shirin bayar da lamuni na shugaban kasa ga masu kanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs).

Manajan Daraktan Bankin Masana’antu (BOI), Dakta Olasupo Olusi ne ya bayyana haka a yayin taron wayar da kan jama’a kan shirin da aka gudanar a ranar Juma’a a Jihar Kano.

Olusi wanda ya samu wakilcin Aminu Yusuf Manajan BOI a Kano, ya bayyana cewa jihar Kano kadai ta dauki mutane 51,033 da suka ci gajiyar tallafin, inda aka kashe sama da Naira biliyan 12.54.

Ya bayyana cewa ana ware Naira biliyan 50 daga cikin asusun shiga domin tallafa wa sana’o’in hannu miliyan daya da suka hada da matan kasuwa, masu sana’a, masu sayar da abinci, telloli da sauran su, tare da tallafin Naira 50,000 a fadin kananan hukumomi 774 na Najeriya.

A cewarsa, shirin ya bayar da rancen kudi har Naira miliyan 5 a kan kashi 9 cikin 100 na ribar da aka samu a shekara, tare da wa’adin shekaru uku ba tare da kudin ruwa ba.

Karanta: Galadima : Sarakunan Kano biyu da ke cikin rikici sun gudanar da bukukuwan naɗi daban-daban

A cewarsa, MSMEs ne ke da kashi 96 cikin 100 na duk kasuwancin da ke Najeriya, suna samar da kashi 84 cikin 100 na ayyukan yi, kuma suna ba da gudummawar kusan kashi 50 cikin 100 ga haɓakar tattalin srziki GDP na kasar nan.

Ya kara da cewa, “A Kano, muna ganin yadda MMEs ke bunkasa tattalin arzikin cikin gida, suna samar da ayyukan yi, samar da ababen more rayuwa, da samar da kirkire-kirkire.”

Ya kuma bayyana ragowar Naira biliyan 75 a karkashin asusun samar da masana’antu (MSF), da nufin tunkarar kalubalen da masana’antun Najeriya ke fuskanta kamar tsadar kayan aiki, gibin ababen more rayuwa, da kawo cikas ga samar da kayayyaki.

A nasa bangaren, Manajan ofishin hukumar kula da kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) na jihar Kano, Bashir Jafa, ya ce hukumar na kara wayar da kan ‘yan kasuwa yadda za su samu tallafin da lamuni.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan shirin mai suna Hauwa Ali, mai zanen kwalliya ta yaba da wannan shirin tare da karfafa gwiwar sauran masu kananan sana’o’i da su yi amfani da wannan damar wajen bunkasa sana’o’insu.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here