Gwamnatin tarayya ta amince da ɗaukar matakan ladabtarwa kan jami’ai 31 na hukumar kula da shige da fice ta Najeriya saboda aikata laifuka daban-daban da suka shafi sabawa ƙa’idojin aiki.
Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, kuma mataimakin kwanturola na hukumar, R. Akinsola Akinlabi, ya fitar a Abuja.
Akinlabi ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa da ke ƙarƙashin hukumar, wanda ya gudanar da taro a ranar 11 ga watan Yuli, 2025.
Ya ce, jami’ai takwas an kore su daga aiki saboda manyan laifuka da suka shafi karya ƙa’idoji, yayin da wasu biyar aka tura su ritaya da tilas saboda rashin da’a a wurin aiki.
Haka kuma, jami’ai takwas an rage musu matsayi daga mukamansu na baya, sannan wasu biyar suka sami gargaɗi a rubuce saboda aikata ƙananan laifuka.
Akinlabi ya ƙara da cewa hukumar ta sake duba ƙorafin wasu jami’ai da aka kora, inda aka dawo da ɗaya bayan an tabbatar da hujjojin sa, yayin da biyu aka sake tabbatar da korarsu.
Ya ce, a wani lamari daban, hukumar ta kuma kori ma’aikata biyu bayan an tabbatar da su da laifin haɗin baki wajen satar makamai da sace mutane, tare da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
Wannan matakin na ladabtarwa ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, da kuma kwanturola janar ta hukumar, Kemi Nandap, domin tabbatar da gaskiya, da’a, da bin ƙa’ida a aikin gwamnati.
NAN












































