An kashe mutane akalla 20, tare da raunata daruruwa a harabar majalisar dokokin Iraqi sakamakon rikici tsakanin magoya bayan fitaccen malamin Shia din nan Muqtada al-Sadr da jami’an tsaro.
A jiya Litinin ne malamin wanda hadakar siyasarsa ta yi nasarar cin kujeru mafiya yawa a zaben majalisar dokokin kasar, ya sanar da yin ritaya daga harkokin siyasa, tare da rufe dukkanin ofisoshinsa abin da ya harzuka magoya bayansa suka je suka mamaye fadar shugaban kasar.
Daman tun a watan Yuli da Agustan nan magoya bayan malamin suka yi kaka-gida a wajen ginin majalisar dokokin kasar don nuna rashin jin dadinsu da kin kafa sabuwar gwamnati.
Ana samun rahotanni rikici tsakanin kungiyoyi masu gaba da juna a biranen Basra da Nasiriya da Hillah.
Kamfanonin sufurin jirgin saman a yankin sun dakatar da zira-zirga.
‘Yan siyasar kasar da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Hadakan Musulmi, da Amurka sun yi kira da a kwantar da hankali
Moqtada al-Sadr, malamin Shia mai tsattsauran ra’ayi wanda yake da miliyoyin mabiya, ya sanar da matakin nasa ne a shafin Twitter.
Daruruwan magoya bayan malamin sun yi zaman dirshan a wajen ginin majalisar dokokin kasar ta Iraqi tsawon makonni bayan da tun farko suka mamaye ginin domin nuna kin amincewa da matakin kin kafa sabuwar gwamnatin.
Malamin ya yi sanarwar ne kwana biyu bayan ya yi kira ga dukkanin wadanda ke da alaka ko hannu a siyasar kasar bayan mamayar da Amurka ta yi wa kasar a shekara ta 2003 da su fice daga fagen siyasar.













































