Babban alƙalin kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, John Tsoha ya canja alƙalin da ke shari’ar jagoran ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, kamar yadda shafin intanet na tashar Channels ya ruwaito.
Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.
A baya dai mai shari’a Binta Nyako ce take sauraron shari’ar, wadda ake zargin Kanu da cin amanar ƙasa da tayar da zaune tsaye.
A watan Satumban shekarar da ta gabata ne Kanu ya buƙaci mai shari’a Nyako ta sauka daga jagorancin sauraron shari’ar, inda ya zarge ta da rashin adalci.
BBC