Amurka ta kora ƴan Najeriya, Gambiya da wasu kasashen Yammacin Afrika zuwa Ghana

Deportees new new

Ghana ta fara karɓar ‘yan yammacin Afrika da aka kora daga amurka, ciki har da ƴan Najeriya da Gambiya, kamar yadda shugaban ƙasar ghana, John Dramani Mahama ya bayyana.

Rahoton Reuters ya nuna cewa an riga an saukar da rukuni na farko da ya haɗa da mutum 14 a birnin Accra, kuma hukumomin Ghana na sauƙaƙa musu dawowa ƙasashensu.

Mahama ya bayyana cewa amurka ta nemi Ghana ta karɓi waɗannan baƙin da ake kora daga ƙasar, inda suka amince da shirin kasancewar ‘yan yammacin Afrika na iya shiga Ghana ba tare da biza ba.

Ya ce hakan ya dace domin tuni tsarin ƙasashen yammacin Afrika ya ba su damar shiga Ghana cikin sauƙi.

Karin labari: Sojojin ruwan Maroko sun ceto baƙin haure ƴan Afirka 141

Wannan shiri ya zo ne a lokacin da gwamnatin shugaban amurka Donald Trump ta ƙara tsaurara manufofin shige da fice, inda ta yi amfani da tsarin mayar da baƙi zuwa ƙasashe uku.

Wannan ya haɗa da korar wasu baƙi zuwa Eswatini, Sudan ta kudu da Rwanda duk da koke-koken ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam.

Sai dai Najeriya ta nuna adawa da irin wannan tsari.

A watan Yuli, ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa gwamnati ba za ta karɓi ‘yan ƙasashen waje da aka kora daga amurka ba saboda dalilan tsaro da tattalin arziki.

Rahotanni sun ce a ranar 9 ga watan Yuli, Trump ya gayyaci shugabannin kasashen yammacin Afrika guda biyar zuwa fadarsa ta White House, inda ya yi ƙoƙarin shawo kansu su karɓi waɗanda ake korowa daga wasu ƙasashe.

Shugabannin da suka halarci taron sun haɗa da na Gabon, Guinea-Bissau, Liberia, Mauritania da Senegal.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here