Hukumar kula da yiwa Malamai Rajista ta Najeriya (TRCN) ta bayyana cewa rashin malamai masu cancanta a makarantu na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke haddasa raguwar ingancin ilimi a ƙasar.
Shugabar Hukumar, Dakta Ronke Soyombo, ta bayyana hakan ne yayin wata hira a tashar talabijin ta Channels, cikin shirin “The Morning Brief”, a ranar Litinin, a wani ɓangare nybikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2025.
Soyombo ta bayyana cewa akwai malamai da ke koyarwa ba tare da takardar cancantar koyarwa ba, musamman a makarantu masu zaman kansu, yayin da wasu ke da sha’awa amma ba su samu damar shiga aikin koyarwa saboda rashin cancanta.
Ta ce hukumar tana ɗaukar matakai don magance ƙarancin malamai ta hanyar samar da tsarin horo na gaggawa domin waɗanda ke da ƙwarewa amma ba su da takardar ilimin koyarwa, inda za su kammala cikin watanni shida.
A cewarta, TRCN ta riga ta yi rajistar malamai kusan miliyan 1.4, kuma burinta a cikin shekaru biyu masu zuwa shi ne ta kai malamai miliyan 20 ta hanyar tsarin amfani da na’urar zamani da ta ƙaddamar.
Karanta: Gwamnatin tarayya ta sake jaddada ƙudirinta na inganta walwalar malamai
Soyombo ta ce aikin koyarwa yana buƙatar haɗin kai tsakanin malamai domin samun nasara, inda ta jaddada muhimmancin tsara darussa tare da musayar dabaru tsakanin malamai da makarantu don inganta ilimi
Haka kuma ta ce gwamnati na ƙoƙarin ƙara yawan malamai ta hanyar bayar da tallafi da kayan koyarwa domin ƙarfafa waɗanda ke cikin harkar da kuma jawo sabbin malamai su shiga harkar koyarwa a ƙasar.













































