Shugaban Majalisar dokokin jihar Kebbi Muhammad Usman Zuru, ya rasu a wani asibiti da ke ƙasar Masar bayan fama da rashin lafiya.
Marigayin ya rasu ne a daren ranar Litinin bayan shafe wani lokaci ya na jinya, kamar yadda majiyoyin kusa da gwamnatin Jihar ta Kebbi suka tabbatar, duk da cewa ba a bayyana takamaiman cutar da ta yi sanadiyyar rasuwar tasa ba.
Zuru, wanda shi ne wakilin mazaɓar Zuru, ya kasance gogaggen ɗan majalisa kuma muhimmin jigo a ɓangaren dokoki na jihar, inda ya taka rawa wajen tafiyar da harkokin majalisar.
Mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin sadarwa da dabaru, Idris Zuru, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da za a jima ba a manta da shi ba.
Ya ce, “Rasuwar Rt. Hon. Muhammad Usman Zuru ta zo mana da matuƙar kaduwa. Babban rashi ne ba ga Kebbi kaɗai ba har ma da ƙasa baki ɗaya.”
Ya ƙara da cewa, gwamnati na ci gaba da tattara cikakkun bayanai, kuma za ta fitar da sanarwa a hukumance tare da sanar da yadda za a gudanar da jana’izarsa bayan tuntubar iyalai da dangin marigayin.













































