EFCC ta kwato fiye da naira biliyan 500, ta samu masu laifi sama da 7,000 cikin shekaru biyu – Tinubu

EFCC and NJIC workshop 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta samu nasarar karɓo kadarori da kuɗaɗe da kimarsu ta haura naira biliyan 500 tare da samun hukuncin laifi sama da mutum dubu bakwai cikin shekaru biyu na mulkinsa.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron horas da alƙalai karo na bakwai wanda hukumar EFCC tare da cibiyar horar da ma’aikatan shari’a ta ƙasa suka shirya a birnin Abuja.

Shugaban ƙasar wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya ce wannan ci gaba alama ce ta jajircewar gwamnatinsa wajen yaƙi da cin hanci da kuma tabbatar da cikakken ‘yancin bangaren shari’a.

Tinubu ya bayyana cewa kuɗaɗen da aka karɓo ana karkata su ne zuwa shirin tallafin zamantakewa, da suka haɗa da lamunin ɗalibai da tsarin ba da rance ga masu amfani da kayayyaki.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba ta taɓa tsoma baki a harkokin hukumomin yaƙi da cin hanci ko kuma shari’a ba, domin an bar su suna gudanar da aikinsu bisa ga dokokin ƙasa.

Shugaban ƙasar ya kuma jaddada cewa babu wani ɗan siyasa ko rukuni da gwamnatinsa ta ke karewa saboda alaƙar siyasa, yana mai cewa ana ba wa bangaren shari’a cikakken ‘yanci domin tabbatar da adalci a cikin al’umma.

A yayin jawabi ga alƙalai, Tinubu ya amince da cewa jama’a na nuna damuwa kan jinkirin da ake samu wajen yanke hukunci a manyan shari’o’in cin hanci, yayin da ake kammala shari’o’in damfara ta intanet cikin gaggawa.

Ya kuma ce lokaci ya yi da za a ƙarfafa tsarin shari’a domin dawo da amincewar jama’a.

Tinubu ya kuma jawo hankalin alƙalai da su kare mutuncin tsarin shari’a wanda ya bayyana a matsayin “mafakar lamirin al’umma.”

Ya ce al’umma na kallon adalcin ƙasa ne ta fuskar shari’a, don haka ya zama wajibi a ba ta kulawa da girmamawa.

A cewar sa, laifukan kuɗi na ci gaba da samun sabon salo, don haka akwai bukatar alƙalai su ci gaba da koyo da sabunta ilimi kan sabbin dabarun da ake amfani da su, musamman a fannoni irin su shaida ta hanyar imel da ma’amaloli na intanet.

Ya jaddada cewa Najeriya mai tsabta daga cin hanci za ta yiwu ne idan kowa ya tsaya wajen yin adalci da gaskiya a matsayinsa na ɗan ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here