Gwamnatin jihar kano ta bayyana cewa dalilinta na rushe shataletalen gidan gwamantin jihar shine rashin ginashi da inganci da akai kuma zai iya ruguzowa a kowa ne lokaci daga wannan shekarar ta 2023 zuwa 2024.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Laraba.
Ya ce Gwamnatin jihar ta tun-tube kwararu da masana aikin gine-gine kafin ta rushe wannan shataletale, kuma sun tabbar da cewa ginin zai iya ruguzowa a kowane lokaci.
“Wannan shataletale ya yi tsayi sosai a sashi a gaban gidan gwamnati, kuma yana barazana ga harkokin tsaron gidan gwamantin.”
“Haka kuma yana kawo cinkoson abubuwan hawa a kofar gidan gwamnati, saboda yayi girma tare da fadi a gurin”
Sanarwar ta kara da cewa rushe gurin ya zama dole ne domin a rage masa tsaye da kuma fada domin hakan shine mafuta da kuma masalaha ta al’umar jihar Kano.













































