Alhaji Bukar Dalori ya zama shugaban riƙo na jam’iyyar APC na ƙasa

Bukar Dalori 750x430

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa, Alhaji Bukar Dalori, ya zama shugaban riƙo na jam’iyyar na kasa.

Hakan ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban jam’iyyar ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi ne a yau Juma’a.

Sashe na 14 (2) na Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyyar APC wanda aka yi wa kwaskwarima, ya tanadi ayyukan Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na kasa, daga ciki akwai taimaka wa shugaban Jam’iyyar na kasa wajen gudanar da ayyukansa.

A sashe na 14 (2)(iii), kundin tsarin mulkin ya bayyana cewa, “Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa zai yi aiki a matsayin shugabanta na kasa idan babu shugaban daga shiyyarsa”.

Ko da ya ke har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a bayyana musabbabin murabus din Ganduje ba, sai dai kawai wani jigo a jam’iyyar ya shaida wa Vanguard cewa, “Eh gaskiya ne, ya yi murabus”.

Yayin da aka ruwaito cewa, tun da farko hadimansa sun kwashe abubuwan da ya shafi kayayyakin Ganduje daga ofishinsa da ke sakatariyar kasa, da alama akwai rudani a harabar yayin da ma’aikata da maziyartan suka samu labarin cikin kaduwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here