Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ramalan Mukhtar Yero, Sanata Shehu Sani, da Sanata Sunday Katung sun yi nasara a zaben fidda gwanin Sanatoci na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna gabanin babban zaben 2027.
Yero ya lashe zaben fidda gwanin Sanatan Arewacin Kaduna na APC da kuri’u 6,060 inda ya kayar da Muazu Mukaddas wanda ya samu kuri’u 1,044, yayin da Bala Ikara ya samu kurii’u 362.
Haka kuma, Shehu Sani ya samu nasara a zaben fidda gwanin Sanatan Kaduna ta Tsakiya bayan ya samu kuri’u 9,105.
Jami’ar zaben kuma mai alhakin bayyana sakamako, Samira Jibrin, ta sanar da cewa Yusuf Zailani ya samu kuri’u 1,021, yayin da Shettima Yerima, wanda ya janye daga takarar, ya samu kuri’u 1,253.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan zaben, Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna kan goyon bayan da suka ba shi.
A halin da ake ciki, Sanata Sunday Katung, shima ya yi nasara a zaben fidda gwanin Sanata a Kudancin Kaduna na APC bayan ya kayar da tsohon Sanata Danjuma Laah da Michael Ayuba.
Da yake sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamako da ke Ƙaramar Hukumar Jema’a, Jami’in zaben kuma mai alhakin bayyana sakamako, Farfesa John Laah na Jami’ar Kimiyya da Aiyuka ta Tarayya, Kachia, ya bayyana zaben a matsayin na lumana, a bayyane kuma abin yarda.
A cewarsa, Katung ya samu kuri’u 7,453 inda ya kayar da Laah wanda ya samu kuri’u 1,370, yayin da Auta ya samu kuri’u 878.
(NAN)











































