Abu Al-Minuki: Yadda farmakin ya gudana, ba a kashe soja ko daya ba – Hedkwatar Tsaro

Army Army 700x430

Hedkwatar Tsaron Kasa (DHQ), ta ce babu wani sojan Najeriya da ya rasa ransa a lokacin farmakin da aka kashe kwamandan ‘yan ta‘adda, Abu Bilal Al-Minuki.

Daraktan Yada Labaran Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar yayin wata hira da aka yi da shi a wani shiri na talabijin wanda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya rawaito.

Onoja ya bayyana farmakin a matsayin hari na musamman da aka tsara sosai kan wani babban Dan Ta’adda da ake nema ruwa a jallo a cikin ‘yan ta’adda.

Ya ce farmakin ya nuna kwarewa, tsari da shiri na dabarun sojojin da suka aiwatar da shirin.

“Muna farin cikin bayyana cewa saboda kwarewar sojojinmu, ba a samu wani asarar rai a bangarenmu ba,” in ji Onoja.

Ya ce an tsara kai farmakin ne ta hanyar bayanan sirri cikakku da hadin gwiwar aiki.

A cewarsa, rahotannin da suka gabata game da mutuwar Al-Minuki a 2024 sun dogara ne kan kuskuren gane mutum. Inda ya ce mutumin da aka kashe shi ne ainihin Abu Bilal Al-Minuki, wanda ke amfani da sunaye daban-daban.

Ya kuma bayyana cewa wadannan sunaye sun taimaka wa dan ta’addan wajen guje wa gano shi na shekaru. “Duniya ta dade tana sanya ido akan wannan mutum tun da dadewa,” in ji shi. Inda ya kara da cewa bayanan tsaro sun danganta kwamandan da wasu hukumomi da ke sa ido a duniya.

“Cikin wadanda ke sanya ido akan shi akwai Majalisar Dinkin Duniya, Amurka, Tarayyar Turai da Najeriya,” in ji shi.

Onoja ya ce an shafe watanni na tattara bayanan sirri da suka kai sojoji ga ainihin wurin da dan ta’addan yake.

Ya ce an kaddamar da farmakin karshe ne kawai bayan kwamandoji sun tabbatar da ingantattun bayanan sirri.

Game da tallafin waje, ya ce babu wani sojan waje da ya shiga aikin.

A cewarsa, Amurka ta ba da taimako ne kawai na bayanan sirri da sa ido.

“Babu wani sojan waje da ya sa kafa a kasa a wannan farmakin, abin da muka samu shi ne tallafin bayanan sirri, sa ido, leken asiri da sauran abubuwan da ke karfafa aiki,” in ji shi.

Ya ce Najeriya za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar tsaro na dabaru don yakar ta’addanci.

Onoja ya kuma ce wasu shahararrun jagororin ‘yan ta’adda na ci gaba da kasancewa karkashin sa ido mai karfi, inda ambaci shugaban ‘yan bindiga da ake nema, Bello Turji, musamman.

“Ba zai iya boyewa har abada ba, al’amari ne kawai na lokaci,” in ji shi, yana rokon ‘yan kasa da su taimaki ayyukan soja da bayanan da suka dace akan lokaci. Ya yi kuma gargadin cewa biyan kudin fansa na karfafa cibiyoyin masu aikata laifuka kuma yana tsawaita rashin tsaro.

Ya sake jaddada kudirin sojoji na dawo da zaman lafiya a al’ummomin da abin ya shafa a Najeriya. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here